On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Masu Tafiyarwa ko Daukar Nauyin Haramtattun Matatun Mai a Najeriya zasu Fuskanci sakamako kan Asarar Rayuka da Dunkiya da aka Samu a Imo - Buhari

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA  a jihar ta tabbatar...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana mummunar fashewar da ta afku a  haramtaciyar matatar mai dake jihar Imo amatsayin wani bala'i na  ƙasa baki daya, yana mai cewa Najeriya  na cikin kaɗuwa da tashin hankali.

A cikin wata sanarwa da mai magan da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya umarci hukumomin tsaro na soji da jami’an leken Asiri da su kara azama wajen gudanar da ayyukan kakkabe haramtattun matatun man Fetur dake sassan kasarnan..

Buhari yace wajibi ne a dora alhakin  asarar rayuka da dukiyoyi sanadiyar Iftila’in akan wadanda suke daukar nauyi ko gudanar da haramtattun matatun mai, wanda ya ce dole ne a kama su baki daya kuma su fuskanci hukunci.

Ya kuma bukaci shugabannin al’umma da ‘yan sanda da masu kula da bayanan sirri su kare afkuwar irin hakan a nan gaba..
A wani bangaren kuwa, yawan mutanen da suka gamu da ajalinsu sanadiyar gobarar ya karu zuwa 110..

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA  a jihar ta tabbatar da cewa an samu karuwar mutum 1 a cikin  yawan mutanen da suka mutu zuwa 110.

Shugaban sashen gudanarwa na hukumar bada agajin gaggawa NEMA Mr Ifeanyi Nnaji, yace karin  mutum dayan da aka samu wata mat ace  mai dauke da juna biyu.