On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Mataimakin Shugaban Majalissar Dokokin Jihar Kano Ya Fice Daga APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar APC.

Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na Mazabarsa.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.