On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Matashi Ya Bankawa Masallata Wuta A Kano

An shiga alhini a gidan 'yan Goro dake kauyen Gadan na karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano Inda wani matashi ya bankawa masallata wuta suna tsaka da Sallah Asuba.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kana wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar dan shekara 38 da ake zargin ya bankawa wani masallaci wuta a gidan 'yan Goro dake kauyen Gadan akaramar hukumar Gezawa, inda mutane sama 24 suka jikata da  daban-daban a lokacin da suke tsaka da sallar Asuba. 

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya kunnuwa masallacin wutar ne  saboda jinkirin rabon gado. 

Da yake amsa tambayoyi a hannun ‘yan sanda, wanda ake zargin Shafi'u ya ce matakin da ya dauka yana nufin kai hari ne kan wasu mutanen da ya zarga da yunkurin kwace masa gadon. 

Da yake zantawa da wakilinmu Nura Haruna Mudi ta wayar tarho da safiyar yau, Dagacin kauyen, Abdul’aziz Yahaya ya ce tun da farko an yi zatton abun fashewa aka dasa a masallacin saboda karfin tashin wutar kafin binciken da kwararrun ‘yan sanda suka gudanar wanda ya nuna wuta ce kawai.

Yanzu haka mutane sama da 20 da kuma wasu kananan yara na sashen kulawar gaggawa na asibitin kwararru na Murtala dake birnin Kano suna karbar magani.
....