On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Matawalle Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Hukuncin Kisa Ga ‘Yan Ta’adda

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Jihar Zamfara ya rattaba hannu akan dokar hukuncin kisa ga duk wani dan bindiga da aka samu da laifi a jihar, yayin da aka tanadi hukuncin daurin shekara 20 akan masu taimaka musu da bayanan Sirri.

Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne a ranar Talata a Gusau, jim kadan bayan majalisar dokokin jihar ta ba da shawarar yanke hukuncin kisa ga masu laifukan ta’adanci.

Bayan ya rattaba hannu a kan kudirin dokar hukunta masu aikata laifukan fashi da makami da barayin shanu da kungiyoyin asiri da garkuwa da mutane da kuma laifukan da suka saba wa doka, Matawalle ya ce dokar za ta zama makami wajen gurfanar da masu aikata laifuka a jihar.

Ya kara da cewa jami’an tsaro suna gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban.

Gwamna Bello Matawalle ya rattaba hannu akan wannan sabuwar doka wadda ake sarai zata taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suke addabar jihar, kuma suke ci gaba da daukar rayukan fararen hula da be su ji ba su gani ba.

Sabuwar dokar na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnatin Zamfara ta umurci jama’a da su mallaki bindiga domin kare kan su daga Yan bindigar da suka hana su zaman lafiya.