On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Matsalar Tsaro Ce Babbar Barazanar Karancin Abinci A Najeriya - Proff Ibrahim

Tsohon shugaban cibiyar bincike kan harkokin aikin gona ta jami’ar Ahmadu Bello Zaria, farfesa Ibrahim Umar Abubakar, ya baiyana rashin tsaro amatsayin babban dalilin da suke haddasa rashin abinci a kasa.

Masanin ya baiyana haka ne a yayin  da yake gabatar da wata mukala,a yayin wani taro kan aikin gona da  kwalejin Fasahar aikin gona ta  gwamnatin taraiyya dake Hotoro a jihar  Kano   ta shirya.

Farfesa Abubakar  ya kara da cewa aiyukan ‘yan ta’adda  sun gurgunta aiyukan gona kamar noma da  kamun kifi da kuma sauran dabbobi, wanda  hakan yasa abune mai wahalar gaske  yin jigilar kayan da aka noma daga wani bangare zuwa wani sashi na kasar nan.

Da yake zantawa da wakilinmu bashir Faruk Durumin iya, Shugaban kwalejin, Dr Muhammad  Yusha’u Gwaram, ya baiyana cewa  kwararru zasu gabatar da mukaloli kimanin 70  a yayin taron, wadda  za’a wallafa a farkon shekara mai zuwa, domin bayar da gudunmuwa a matayin abun koyo ga Dalibai da kuma sauran kwararru.