On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Matuka Adaidaita Sahu Zasu Baiwa Tinubu Da Gawuna Kuri'a Dubu 500 A Kano

ADAIDAITA SAHU

Hadakar Kungiyar masu tuka baburan Adaidaita Sahu ta jihar Kano, ta yi alkawarin hada kan mambobinta domin su samar da kuri'a dubu 500 ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Apc, Bola ahmed tinubu, da dan takarar gwamnan jihar kano, Dr Nasiru gawuna, a zaben shugaban kasa da na gwamna da za’a yi.

Shugaban kungiyar, Alhaji Mansur Tanimu, shine ya yi wannan  alkawari a ranar Alhamis  a yayin  wata ziyarar ban girma ga shugaban hukumar  KAROTA, wanda ke rike da mukamin daraktan kungiyar  Masu  goyon bayan tinubu ta arewa maso yamma, Baffa Babba Dan Agundi.

Ya ce matakin ya zama dole sakamakon yadda  gwamnati ta  saurari korafe-korafen mambobinta da kuma alkawarin da gwamnatin jihar ta yi na duba hanyoyin tallafa musu domin inganta harkokinsu.