On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Mayakan ISWAP Dana Boko Haram Na Shirin Kai Hare-Hare Wasu Jihohi

ISWAP

Wani binciken sirri ya gano cewa kungiyar mayakan ISWAP dana Boko Haram na shirin kai hare-hare a wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yammacin kasar nan.

Rahotanni na baiyana  cewa hukumomin tsaro sun samu rahotonnin sirri na karkashin kasa dake baiyana cewa mayakan na   ISWAP da Boko Haram sun shirya kai hari jihohin Legas, Kaduna, Kogi, Katsina da Zamfara da kuma Abuja  babban birnin tarayya.

Wata sanarwa da ta fita daga shalkwatar Rundunar tsaro ta CIVIL DEFENCE, a ranar Talata,  ta sanar da  jihohin da abun ya shafa  kan yiyuwar  kai masu hare-haren,  To Sai dai  kuma  kakakin hukumar Shola Odumosu, ya musanta cewa  wasikar  daga  wajensu  ta fitar.

Sai dai wani kwamandan rundunar dake waa jiha a kasar nan, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar wa jaridar Punch takardar da rundunar ta fitar,  ya ce an umurci jami’an tsaro da su yi gum da bakinsu  domin kada  al’amarin ya haifar da rudani a tsakanin jama’a.

 

More from Labarai