On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mun Dawo Daga Rakiyar Dogaro Da Aikin Gwamnati - KASOSA

Mambobin Kungiyar KASOSA

Kungiyar tsoffaffin daliban makarantun kimiyya a jihar Kano KASOSA, ta ce ta dawo daga rakiyar dogaro da aikin gwamnati inda zata fara koyawa mambobinta sana'o'i duk da fasahar da su ke da ita domin kaucewa dogaro da aikin gwamnatoci.

Shugaban kungiyar na jahohin Kano da Jigawa Alhaji Balarabe Nuhu Jallah Danbatta,  ya bayyana hakan yayin taron buda baki da kungiyar ta shirya karo na 10 domin sada zumunci a tsakanin mambobinta da ya gudana a birnin Kano.

Jallah ya ce kaso 90 cikin 100 na likitoci da sauran ma'aikatan kiwon lafiya da  ke aiki a asibitocin Jahohin Kano da Jigawa makarantun kimiya ne suka yaye su, yana karawa da cewa duba da halin da Najeriya ke ciki ya zama wajibi su tashi tsaye wajen koyawa Mambobinsu sana'o'in dogaro da kai domin kaucewa dogara da aikin gwamnati.

Wakilin mu ya rawaito cewa  taron ya samu halarttar malaman makarantun kimiya da tsoffaffin dalibai da sauran daruruwan Mlmambobin kungiyar ta KASOSA daga sassa daban-daban na Najeriya.