On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Muna Maraba Da Majalissar Bada Shawara A Jihar Kano - Mallam Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekaro ya ce har yanzu gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta tuntube shi ba kan kwamitin dattawa ko ba da shawara da aka  samar. 

Shekarau wanda shine Sardaunan Kano, ya bayyana hakan ne ta cikin wani shiri  kai tsaye da Arewa Radio a daren jiya. 

Da yake yabawa Gwamnan kan wannan shiri, Shekaru ya ba da shawarar cewa a fadada aikin kwamitin fiye da tsaffin gwamnoni domin hadawa da sauran masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na jihar.

 Ya ce a shirye ya ke ya amsa gayyatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin amfanin jihar Kano da  al’ummarta tunda an kammala yakin neman zabe.