On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Muna yiwa al-ummar Kano ta tsakiya albishir da ayyukan raya 'kasa a cikin kasafin Kudin 2024 - Sanata Hanga

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Rufa'i Sani Hanga yace yana cigaba da samun sauki sosai bayan shafe sama da wata 7 yana Jinya.

Duk da cewa ya fuskanci kalubalen rashin lafiya bayan zabensa, wanda ya kai ga jinya a gida Najeriya da kasashen waje, Sanata Hanga ya ce ya jajirce wajen yiwa al'ummar mazabarsa hidima.

Yayin wani taron manema labarai a karon farko bayan nasarar zaben 2023 karkashin Jam'iyyar NNPP, sanata Hanga ya kuma jaddada kokarinsa na ganin an samar da ayyuka daban-daban a yankinsa, tare da jaddada aniyarsa na bibiya sanya ido sosai kan aiwatar da su.

A yayin da yake ci gaba da samun sauki da kuma kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Sanata, Hanga ya ce zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen bibiyar hukumomin da suka dace wajen aiwatarwa.