On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Murya: Abubuwan da Gwamnatin Kano Ta Yi a Bangaren Kiwon Lafiya Cikin Shekara 1 – Dr. Labaran

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta dukufa wajen tabbatar da cewa ta samar da nagartattu kuma wadatattun likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya domin cike gibin da ke da akwai a asibitocin gwamnati dake fadin jihar.

Kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan albishir a lokacin da yake ganawa da manema labarai a wani bangare na bikin cikar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf shekara guda da kafuwa.

Dr. Labaran ya zargi gwamnatin baya karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da shafe shekaru akalla biyu ba tare da ta dauki likita ko da guda ba, duk kuwa da cewa akwai ‘ya’yan jihar Kano sama da 300 da suka kammala karatun su na likita ba tare da aikin yi ba, al’amarin da yace ya kara ta’azzara karancin likitoci da ake fama da su.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa karbar mulkin su ke da wuya, gwamna ya sahalewa ma’aikatar lafiya ta jiha da ta fara daukar likitocin aiki domin rage gibin da kuma tabbatar da cewa matasan likitocin sun samu aiyukan yi da kuma kwarewar da suke bukata.

“Mun fara daukar wannan likitoci ne da guda talatin da biyar-biyar, kuma yanzu haka za mu koma guda hamsin-hamsin har sai mun tabbatar da cewa ba wani dan asalin jihar Kano da ke da takardar kammala karatu a fannin likitanci da ba shi da aiki.”

“Haka kuma mun dauki likitoci masu matakin kwarewa na biyu da ake kira da Medical Officers a turance guda 70, sannan muka kara daukar wasu sababbi guda 29 a baya-bayan nan, kafin mu sake daukar ma’aikatan jinya guda 70, duka domin inganta harkokin bada kulawar lafiya karkashin wannan gwamnati.”

Kwamishinan lafiyan, ya kuma yi Karin haske dangane da yanayin da makarantun da ke horas da ma’aikatan lafiya suka tsinci kawunan su a ciki kafin zuwan gwamnatin ta su, inda yace makarantar horas da ma’aikatan jinya da ungozoma ta jihar Kano ta shafe shekaru ba tare da hukumomi sun tantance kwasa-kwasai da take koyar wa ba (accreditation).

A cewar sa, yanzu hakan ya riga ya zama tarihi tare da bada tabbacin cewa makarantar na nan tana cigaba da aiki yadda kamata tare da tabbatar da cewa ana daukar dalibai ne bisa cancanta kawai.

Daga nan sai ya kara da cewa, la’akari da tulin matsalolin da gwamnatin jihar ta gada a fannin kiwon lafiya, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi wajen ware kudi mafi tsoka a tarihin jihar Kano ga bangaren, daga naira biliyan 40 da doriya kamar yadda ake a da, zuwa sama da naira biliyan 7.

Kwamishinan yace wasu daga cikin aiyuka da gwamnatin ta gudanar sun hadar da;

  • Kwato asibitin yara na Hasiya Bayero daga hannun wadanda aka cefanar wa, sabunta shi da kuma bada magunguna ga marasa lafiya kyauta a cikin sa.
  • Gyara da kuma sabunta sashen bada agajin gaggawa na asibitin Murtala Mohammad
  • Gyaran asibitin yadakunya a karon farko tunda aka assasa shi
  • An kammala gyaran asibitin Nuhu Bamalli, yayinda ake jiran wadata shi da kayan aikin da yake bukata kafin gwamna Abba ya bude shi
  • Dakin gwaje-gwaje na Occupational Hazard and Environmental Health

Dr. labaran, ya alakanta ta’azzarar da cutar nan ta mashako, wacce ta fi Kamari a jihar Kano a lokutan baya da sakaci wajen samar da alluran rigakafi domin bawa kananan yara kariya daga ire-iren wadannan cututtuka masu yaduwa da hadarin gaske.

A bayanin sa, gwamnatin Kano ta samar da isassun alluran rigakafin cututtuka dake addabar al’uma, musamman ma kananan yara, yana mai cewa hakan ya taimaka matuka wajen tabbatar da cewa an bawa al’uma kariya daga kamuwa daga cututtuka.

“A yau wannan cuta ta mashako da sauran cututtuka dake barazana ga rayuwar al’ima na dap da zama tarihi saboda kokarin gwamnati na samar da wadatattun alluran rigakafi.”