On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane 26 Sun Mutu Sakamakon Gobarar Daji A Kasar Algeriya

GOBARAR DAJI

Kimanin mutane 26 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wata gobarar daji da ta lakume gundumomi 14 na arewacin kasar Aljeriya a ranar Laraba.

Ministan cikin gida na kasar, Kamel Beldjoud ya fadawa  gidan talabijin na kasar cewa mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a yankin  El Tarf da ke kusa da kan iyaka da kasar  Tunisia, baya ga wasu biyu da suka mutu tun farkon tashinta a yankin  Setif.

Hukumar kare hakkin farar hula a yankin  Setif tace  wasu mata biyu, Wadanda suka hada da wata Uwa  mai shekaru 58 da Yarta  mai shekaru 31  sun mutu a yankin sakamakon ibtila’in Gobarar Dajin.

Kazalika a yankin  Souk Ahras wanda ke iyakar kasar  Aljeriya da Tunisia daga gabashin kasar,  an ga mutane na ficewa  daga gidajensu yayin da gobarar ta bazu kafin jirage masu  saukar ungulu na kashe gobara su karasa yankin.

Tun a farkon watan Agusta da muke ciki ne, Aka samu tashin gobarar  Daji har  Dari da Shida a kasar  ta Algeriya.