On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Mutane 372 Ne Suka Mutu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa A Jahohi 33 Na Najeriya Da Kuma Birnin Abuja

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin ‘yan Najeriya 372 a jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya cikin watanni takwas da suka gabata.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa Mustapha Habib Ahmed shine ya bayyana haka jiya a Abuja yayin kaddamar da sabbin motocin aiki da na’urori na musamman ga hukumar NEMA.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai fadar shugaban kasa ta ce tun daga watan Janairu, ambaliyar ruwa ta kashe mutane 115 tare da raba mutane  dubu 73 da 379 da muhallansu tare da jikkata wasu 277 a jihohi 22 da babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai shugaban hukumar ta NEMA a jiya ya ce: “A cikin watanni takwas da suka gabata, ambaliyar ruwa ta mamaye jihohi 33 cikin 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, al’amarin da ya shafi mutane sama da dubu dari biya da takwas tare da sanadiyar mutuwar mutane kusan 372 sai 277 da suka  jikkata.

Jahohin Sokoto, Jigawa Kano da Naija na fama da matsananciyar ambaliyar ruwa a kwanakin baya-bayan nan.

More from Labarai