On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mutane 603 Ne Suka Mutu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa A Najeriya - Sadiya Faruk

Ma’aikatar jin kai ta ta fitar da sabbin alkaluman na yawan adadin mutanen da suka mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Najeriya.

Ministar ma’aikatar Sadiya Farouk, ta ce yawan mutanen sun kai 603.

Haka kuma anyi  kiyasin cewa mutane fiye da miliyan daya da dubu 300 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa a fadin kasar.

Ministar ta ce: ”Akwai wadanda suka ji raunuka sakamakon ambaliyar wanda yawansu ya kai 2,407,, sannan kuma akwai gidaje dubu 121, 318 da ambaliyar ta shafa.”

Sadiya Farouk, ta ce akwai kuma gidaje fiye da 82,000 da suka rushe gaba ɗaya.

Ministar ta ƙara da cewa sakamakon abin da ya faru a bana, akwai matakan da ya kamata a dauka na kauce wa samun irin wannan mummunar asara, kamar kwashe mutanen da ke zaune a yankunan da ke gabar ruwa.

Karin Magana: Dutsen Dake cikin Ruwa Bai san ana Rana ba