On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Mutane Dubu 70 Ne Suka Nemi Aikin Koyarwa A Jihar Kaduna

GWAMNA EL-RUFA'I NA JIHAR KADUNA

Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna ta tabbatar da cewa mutane akalla dubu 73 ne suka nemi aikin koyarwa a makarantun firamare wanda a baya hukumar ta sanar zata dauki mutane dubu 10.

Shugaban hukumar Alhaji Tijjani Abdullahi ne ya bayyana hakan a yau, a lokacin da aka fara rubuta jarabawa ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa ga wasu daga cikin mutanen da aka zaba daga cikin masu neman aikin a jami’ar jihar Kaduna.

Abdullahi wanda Mubarak Mohammed jami’in hukumar ya wakilta, yace ana gudanar da jarabawar ne bi da bi a cibiyoyi dake Kaduna da Zaria da Kafanchan.

Yace jarabawar wadda aka fara a ranar 17 zuwa 28 ga watan nan da muke ciki, za’a yita ne cikin tsanaki, yana mai cewa mutane masu kwazo kuma wadanda suka cancanta ne kawai za’a dauka aikin.