On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane Kusan Dari Takwas Sun Kamu Da Cutar Mashako A Najeriya - NCDC

Cibiyar  dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta ce mutane 798 ne aka tabbatar sun kamu da cutar mashako da ake kira diphtheria tare da mutuwar mutane 80 a fadin jihohi takwas ciki har da babban birnin tarayya Abuja tun farkon wannan shekarar ta 2023.

A wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun babban daraktan ta, Dr Ifedayo Adetifa, ta ce an samu bullar cutar a fadin kananan hukumomi 33 na jihohin da abin ya shafa.

Sanarwar ta ce akasarin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga Kano da Legasda  Yobe da Katsina da Cross River da  Kaduna, da Osun.

Ya ce, kashi 71.7 na mutane  798 da aka tabbatar sun kamu da cutar suna  tsakanin yara masu shekaru 2 zuwa 14.

Ya zuwa yanzu, an samu adadin mutuwar mutane 80 da aka tabbatar sun kamu da adadin wadanda suka mutu wanda  ya kai kashi 10.

NCDC ta ce tana kuma sane da mutuwar wata yarinya mai shekaru hudu sanadiyar cutar diphtheria a Abuja a watan da ya gabata.