On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Mutane Sama Da Talatin Sun Mutu A Sakamakon Hadarin Mota A Kan Hanyar Zariya Zuwa Kano

HADARI

Kimanin mutane 30 ne suka mutu a wani kazamanin hadarin mota da ya faru akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Alhamis.

Hadarin ya  faru ne  da misalin karfe 5 da Rabi  na  yammacin Ranar Alhamis a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.

Wani shaidar gani da ido Suleiman Mohammed ya ce sakamakon wutar da ta kama motocin da abin ya shafa, da kyar mutane suka iya ceto  6 daga  cikin  wadanda lamarin ya rutsa da su.

Mataimakin kwamandan hukumar kare  afkuwar  hadurra ta kasa   mai kula da shiyyar Zariya,  Abdurahman Yakasai ya tabbatarwa manema labarai faruwar hatsarin.

Ya ce hadarin  ya ritsa  da wasu   motocin bas kirar Toyota masu cin mutane  18 da kuma wata mota kirar  Volkswagen Gulf.

 Ya kuma ce a yanzu haka ana kan binciken gano bayanan wadanda  hadarin ya ritsa dasu, bayan wutar data kama motocin ta kone su baki dayansu.

More from Labarai