On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

NAFDAC; Kasashen Ketare Na Watsi Da 70% Na Kayan Abinci Da Ake Fitarwa Daga Najeriya

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ce sama da kashi 70 cikin 100 na kayan  abincin da ake fitarwa daga Najeriya ana ki amincewa da su a kasashen waje.

Babbar daraktar hukumar, Mojisola Adeyeye, ta koka da cewa al’amarin na janyo hasarar makudan kudade ga masu fitar da kayayyaki da ma kasa baki daya.

Da take jawabi a wajen kaddamar da sabon ofishin hukumar NAFDAC a filin jirgin sama na Legas, Adeyeye ta ce nan ba da dadewa ba kin amincewar zata  zama tarihi idan aka karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumar ta NAFDAC da sauran hukumomi a tashoshin jiragen ruwa.

Ta ce, NAFDAC za ta tabbatar da kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje suna da inganci da kuma cika ka’idojin kasashen da ake kaiwa  kafin ma kunshe su.