On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

NAHCON Ta Aike Da Tawaga Kasar Saudiyya Domin Dakile Karin Kudin Kujerar Hajji 2023

Akwai fargabar cewa ana iya samun karin kudin aikin Hajjin bana fiye da yadda aka saba, biyo bayan karin farashin masaukai a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Hakan na zuwa ne sakamakon yadda aka rushe  galibin gidajen da ake kamawa mahajjatan Najeriya, karkashin sabon shirin  fadada garin na Makkah.
Wannan na zuwa ne a yayin da ake sa ran sama da mahajjata miliyan 3 za su gudanar da aikin hajjin na bana, sabanin alkaluman mahajjata na  shekarar da ta gabata inda  kusan Mutane miliyan 1 suka samu damar halartar ibadar a Kasar ta saudiyya, wanda hakan ya sa ake samun karancin masauki a Makkah.
A wani mataki na tunkarar matsalar hukumar aikin hajji ta Kasa  NAHCON ta aike da tawaga karkashin jagorancin kwamishina mai kula da harkokin  kudi da ma’aikata na  hukumar Nura Hassan Yakasai, zuwa kasar Saudiyya domin samar da masaukai masu kyau ga maniyyatan da suka shirya zuwa aikin hajji na bana.

Yace tawagar da ta kunshi sakatarorin jin alhazai na jahohi na tattaunawa da masu masaukai da masu ruwa da tsaki  wajen ganin an samo sauki ga Mahajjatan Najeriya.