On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

NAHCON Ta Nanata Dokar Mahukuntan Kasar Saudiyya Kan Shiga RAUDAH

Hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON, tace har yanzu babu rahoton rasa rai ko damfara da aka samu a Kasar Saudi Arabia, daga lokacin fara jigilar Alhazan Najeriya zuwa yanzu.

Jami’in Hukumar mai kula da harkokin Alhazan Najeriya a Madina Sheikh Ibrahim Idris Mahmud, ya tabbatar da hakan a ganawarsa da manema labarai a birnin na  Madina.

Idris Mahmud, ya ce “kawo yanzu jiragen da ke jigilar maniyyatan  Najeriya sun yi jigilar mutane sama da dubu talatin da uku cikin sawu 80) inda tuni sama da dubu goma sha uku suka isa garin  Makka, domin bayar da dama ga shauran maniyyata da ke kan hanyarsu ta zuwa Madina, daga  Najeriya su yi ziyara a Masallacin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)”.

Da yake amsa tambaya akan sabon tsarin kasar Saudi Arabia na yin rijista ga dukkanin wani Alhaji da yake son shiga RAUDAH, kafin shiga.

Sheikh Ibrahim, ya ce “tun a shekarar da ta gabata, ya ce kasar Saudiyya ta sanyya sharadi na neman izi ga kowanne Alhaji,  dake son shiga RAUDAH, ta  harabar cikin Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W) inda yace “hukumomin alhazai a  Jihohin Najeriya , suna da masaniya akan al’amarin”.

Raudah, wuri ne da duk wani maniyyaci da ya sauka a Madina ke da shaukin ya ga ya shiga ciki, domin yin nafila da addu’a bisa la’akari da  fadin fiyayyan haliita da ya ce Raudah, wani yanki ne daga cikin gidan Aljanna.

A yanzu haka dai akwai tarin Alhazai da suka yi rijistar neman shiga Raudah, da ba lallai kowa ya samu damar hakan ba.

Sai dai yace suna ta kokari wajan ganin an bawa Alhazan damar shiga.

Akarshe ya ce Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta cigaba da kokari wajan tabbatar da samun nasarar aikin hajin da ba’a taba samu ba  a shekarun baya.