On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

NAJERIYA : Rikicin Shugabanci Ya Kunno Kai A Majalissar Dokokin Jihar Nasarawa

An samu bayyanar wakilai biyu dake ikirarin samun kujerar jagorantar majalisar dokoki ta 7 a jihar Nasarawa.

Ibrahim Balarabe da Daniel Ogazi dukkansu daga shiyyar yammacin jihar sune wakilan biyu dake ikirarin shugabancin kuma dukkansu ‘yan APC ne.

A jiya Talata 6 ga watan Yuni ne aka shirya kaddamar da majaliisar ta 7 da kuma zaben kakakin majalisar da mataimakinsa amma magatakardan majalissar ya sanar da dage zaben saboda dalilan tsaro.

Daga karshe mambobi 11 ne suka zabi Ibrahim Balarabe da Jacob Kudu a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa a daya daga cikin ma’aikatun jihar inda mukaddashin magatakardar majalisar Ibrahim Musa ya rantsar da su.

Amma an zabi Ogazi da Adamu Oyanki a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa da wakilai 13 a harabar majalisar.

Bayan haka Gwamna Abdullahi Sule ya karbi bakuncin Balarabe da Kudu da sauran ‘yan tsaginsa a fadar gwamnatin jihar Nasarawa da ke birnin Lafiya.