On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

NNPP Ta Kafa Kananan Kwamitoci 31 Kan Shirin Karbar Mulki A Kano

Kwamitin karbar mulki na jam’iyyar NNPP a jihar Kano ya fitar da jerin sunayen kananan kwamitoci 31 na bangarori daban-daban da kuma sassan tsarin mika mulki.

Shugaban kwamitin Dr Abdullahi Baffa Bichi, wanda ya bayyana sunayen kananan kwamitocin a ranar Alhamis, ya ce tsarin mika mulki zai aiki tukuru don ganin an yi nazari da kuma rubuta duk abin da aka gada daga hukumomi da ma’aikatun gwamnati  yadda ya kamata.

Wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna mai jiran gado ya fitar, ta lissafa kananan kwamitocin da suka hada dana  Ilimi da Kiwon Lafiya da dawo da dukiyoyin Jama’a da Ayyuka da  Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a sai Gidaje da Sufuri.

Haka kuma akwai Muhalli da Yanayi da  Kudi tare da Kasafin Kudi da Tsarin Tattalin Arziki da kuma  Albarkatun Ruwa.

Dr Bichi ya bukaci dukkan mambobin kwamitoci daban-daban da su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da kwazo da cikakkiyar  kwarewa wajen gudanar da ayyukan.