On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

NULGE Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Farfado Da Kananan Hukumomi A Najeriya

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauki matakin gaggawa domin magance tabarbarewar harkokin kananan hukumomi.

Shugaban kungiyar, Ambali Olatunji ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja a wajen bikin makon NULGE na kasa.

A cewarsa, bikin na bana na da nufin jawo hankalin duniya game da tabarbarewar tsarin kananan hukumomi wanda a baya ake martabawa  kuma ake aiki akai.

Olatunji ya kuma nunar da cewa dimbin matsalolin da ke addabar al'ummar kasarnan nada alaka da tabarbarewar ayyukan kananan hukumomi da suka fi kusanci ga al’umma.