On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Osinbajo ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar neman shugabancin Najerita-2023

Ya ce yana neman tsayawa takarar  domin inganta rayuwar 'yan Najeriya...


Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yada ta talabijin da sauran kafofin sada zumunta inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce yana neman tsayawa takarar  domin inganta rayuwar 'yan Najeriya  yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa yana da kwarewar shugabanci.

Ya ce a cikin shekara bakwai, ya bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban kasa, ya wakilci kasarnan a muhimman bangarori a kasashen waje. kuma ya  ziyarci kusan kafatanin kananan hukumomin Najeriya da kasuwanni, da masana'antu, da makarantu da gonaki.

Ya kara da cewa ya je gidajen talakawan kasarnan a yankuna daban-daban, sannan ya tattauna da kwararru a bangaren fasaha a Lagos, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaka daga Lagos, Onitsha, da kuma Kano, sannan ya yi  magana da kanana da manyan 'yan kasuwa.

Mataimakin shugaban kasar ya ce ya samu wannan kwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolon Najeriya da kuma yadda zai magance su.

Baya ga kewayawa da zai yi jihohi domin neman magoya baya, 'yan kwamitin yakin neman zaben sa za su shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023.