On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Osinbajo Zai Wakilci Najeriya A Bukin Rantsar Da William Ruto A Matsayin Shugaban Kasar Kenya

Mataimakin Shugaban kasa

A yau ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai tashi daga Abuja zuwa Nairobi na kasar Kenya domin wakiltar Najeriya a wajen bikin rantsar da shugaba William Ruto a matsayin Zababben shugaban kasar Kenya na biyar.

Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, shine ya bayyana hakan  ta cikin  wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Osinbajo zai bi sahun sauran shugabanni a fadin Afirka wajen bikin rantsar da sabon shugaban kasar  a filin wasa na Kasarani da ke Nairobi, inda ake sa ran shugabannin kasashe kimanin  20 ne za su halarci bikin.

Mataimakin shugaban kasar yana tare da karamin  ministan harkokin wajen kasar nan  Amb. Zubairu Dada, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Sen. Babafemi Ojudu.

A ranar Talata ne Osinbajo zai dawo  gida  Najeriya.

 

More from Labarai