On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

PDP tayi Martani Yayinda, Jam’iyyar APC Ke Tattaunawa Da Gwamnan Wike Na Rivers Kan Zaben 2023

Wasu rahotanni na nuni da cewa Jam’iyyar APC na tattaunawa da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers domin ya marawa jam’iyyar baya a babban zaben shekara mai zuwa.

 

Wike da abokansa suna takun saka da shugabancin jam’iyyar PDP tun bayan da ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

A ranar Talata ne gwamnan ya amince tare da nuna goyon baya ga gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas wanda ke jam’iyyar APC, matakin da ya kara dagula rikicin PDP.

Da yake tsokaci kan matakin, wani jigo a jam’iyyar APC Farouk Aliyu ya ce jam’iyyar ta riga tayi nisa a tattaunawa da Wike kuma APC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen maraba da gwamnan zuwa cikinta domin aiki tare a zaben shekara mai zuwa ta 2023.

Sai dai, jam'iyyar PDP ta bakin shugabanta a Legas, Philip Aivoji ya kalubalanci ikirarin cewa gwamna Babajide Sanwo-Olu ya samun goyon bayan  takwaran nasa na jihar Rivers, Nyesom Wike.

Hakan na zuwa ne a lokacin da  Jam'iyyar PDP a jihar Legas ta ce abun damuwa ne yadda gwamna Nyesom Wike ya kira gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC, a matsayin mai taka rawar gani ba tare da tambayar sau nawa ya gayyaci kowa zuwa Legas domin kaddamar da aikin koda Rijiyar Burtsatse ce  ba kusan shekaru hudu yana mulki a matsayin gwamna.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Hakeem Amode, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

A jiya ne Gwamna Wike ya kasance babban bako na musamman a wajen taron shekara-shekara na kwamitin matan jami’an jihar Legas na shekarar 2022 inda ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan dari uku, inda ya yaba da kwazon Gwamna Sanwo-Olu a kan mulki wanda mutane da yawa ke ganin ya goyi bayan gwamna Sanwo Olu a karo na biyu kan mulki.

Ita kuwa Jam’iyyar APC a jihar Rivers ta soki tallafin da gwamna Wike ya bayar a baya-bayan nan.