On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

PENGASSAN Ta Bukaci A Kwace Lasisin Masu Sayar Da Litar Man Fetur Fiye da Kima

Kungiyar manyan ma’aikatan man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya PENGASSAN ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta soke lasisin ‘yan kasuwar man da ke siyarwa  a farashin da ya wuce kima.

PENGASSAN, a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Festus Osifo ya fitar, ya ce kiran da aka yi na janye lasisin, ya biyo bayan karancin man da ake fuskanta a cikin watanni shida da suka gabata.

Yace ya kamata hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa ta gaggauta tura ma’aikatanta a wurare daban-daban domin sanya ido akan yadda ake bin ka’idar sayar da man  kuma duk wanda aka samu yana sayarwa fiye da kima a kwace masa lasisi.

More from Labarai