On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Real Madrid Ta Casa RB Leipzig Da Ci 2 Babu Ko Daya

TAWAGAR YAN WASAN MADRID

Kugiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta caskara RB Leipzig da ci biyu da nema a wasan gasar zakarun cin kofin turai UEAFA da suka yi a daren ranar Laraba.

Dan wasa  Fedrico Velverde ne  ya fara  zura kwallo ta  farko a minti  na  tamanin bayan  dauki ba dadin da suka yi a tsakaninsu da  yan wasan kungiyar  RB Leipzig

Kazalika Dan wasa Marco Asensio ya kara  tabbatarwa da kungiyar ta Real madrid samun nasara a wasan a minti na  91 na wasan bayan da aka yi karin  mintina hudu.

Idan ba'a manta ba a daren  ranar  Talata ne abokin hamaiyyar kungiyar ta Madrid, Bercelona  tayi rashin nasara a hannun Bayern Munich wadda  ta zura mata kwallaye biyu babu ko daya a wasan da suka yi.

A cigaba da bibiyar wannan shafin domin samun cikakken  labarin wasanni da suke faruwa a fadin duniya.

 

More from Labarai