On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Rurum, Kawu Sumaila, Kofa, Jobe sun dira a Kano tare da Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jamiyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya iso Kano tare da wasu jiga jigan mambobin jamiyyar APC dake shirin ficewa daga jamiyyar su koma jamiyyar NNPP.

Wadanda suka iso birnin Kano tare da Kwankwaso a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano sun hadar da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano Alhassan Rurum, sai Bbban daraktan kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasar nan Tinubu, Abdulmumin Jibrin Kofa, da mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tofa da Dawakin Tofa da rimin Gado Abdulkadir Jobe, sai kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammad Buhari shawara kan harkokin majalisa Kawu Sumaila.

Ilahirin tawagar tsohon gwamnan dai sun fice daga jamiyyar APC a kwanan nan, kuma ana kyautata zaton zasu sanar da sauya shekar a hukumace a wata ganawa da ake yi a yanzu haka a gidan kwankwaso dake Miller road.

Sai dai kuma ba’a ga tsohon gwamnan jihar Kano sanata Ibrahim Shekarau ba a cikin tawagar wanda a baya ake saa ran zai dawo tare dasu kuma ya sanar da sauya shekar sa zuwa jamiyyar NNPP.