On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sabon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasa Ibrahim Gusau Ya kama Aiki

SABON SHUGABAN HUKUMAR KWALLON KAFA TA KASA

Wakili a Hukumar Kwallon kafa ta duniya kuma dan kwamitin gudanarwa na Hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Afrika, Amaju Pinnick ya mika ragamar tafiyar da Hukumar Kwallon kafa ta kasa NFF ga sabon shugaban hukumar Ibrahim Musa Gusau.

Gusau ya samu nasara a zaben  shugabannin Hukumar da aka gudanar a ranar  30 ga watan da ya  gabata a birnin Benin na kasar Edo.

Shugaban hukumar mai barin gadoyayi kira ga  jami’an gudanarwa na  hukumar da sauran ma’aikata dasu baiwa  sabon shugaban hukumar cikakken goyon baya kamar yadda suka  bashi a lokacin da yake shugabantar hukumar.

Kazalika yace  kofarsa  zata cigaba da kasancewa a bude domin neman shawara  a duk lokacin da bukatar hakan ta taso

More from Labarai