On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sagagi Ya Bukaci Shugaban PDP Na Kasa Da Mukarrabansa Su Yi Murabus

Shugaban tsagin jam'iyyar PDP a jihar Kano, Shehu Wada Sagagi ya bukaci shugabancin jam'iyyar na kasa karkashin jagorancin Iyocha Ayu da su sauka daga mukaman su.

 

Sagagi ya bayyana hakan ne a yau yayin wata ganawa da manema labarai a Kano.

 

Ya kuma yi bayanin cewa, yayi wannan kira ne domin tunasar da shugaban jam'iyyar ta PDP na kasa cewa yayi alkawarin sauka daga kujerar sa idan har jam'iyyar ta sa ta tsayar da wani dan Arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

 

A cewar Sagagi, hakan zai taimaka wajen sake hada kan jam'iyyar domin samun nasarar ta a zabe mai zuwa.

More from Labarai