On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sakamakon Zaben 2023 : Jam'iyyar PDP Ta Kawar Da APC A Jihar Zamfara

A safiyar yau Talata 21 ga watan Maris 2023 hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Dauda Lawal Dare na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Zamfara da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Jami’in tattara sakamakon zabe na INEC, Kassimu Shehu, ya ce Dauda  Lawal ya samu kuri’u dubu 377 da 726 masu daga kananan hukumomi 14.

Shehu ya ce dan takarar gwamna na PDP ya doke Gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u dubu 311 da 976.

Idan za’a iya tunawa dai tunfa farko Matawalle  ya zama gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP kafin ya sauya sheka zuwa APC, aka tsige mataimakinsa a lokacin Barr. Madi Aliyu Gusau, wanda ya ki bin sa.