On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Samar Da Ma'aikatar Kula Da Harkokin Addinai Zai Taimaka Wajen Hadin Kan 'Yan Najeriya - Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya samar da ma’aikatar harkokin addinai a matsayin hanyar samar da matakan magance rashin jituwa tsakanin  addinai a fadin kasar nan.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a Kano yayin kaddamar wani littafi da tattaunawa tsakanin mabiya addinai da kungiyar ActionAid Nigeria ta shirya domin dakile tsatstsauran ra’ayi.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Hakimin Nassarawa, Alhaji Aminu Babba ‘DanAgundi, ya bukaci Tinubu ya yi koyi da Gwamna Abdullahi Ganduje wajen samar da ma’aikatar harkokin addinai domin Kano ta samu kwanciyar hankali a cikin shekaru 8 da suka gabata.

A nata jawabin, shugabar kungiyar ActionAid Najeriya, Ene Obi ta ce an samar da littafin ne domin samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Kano.

More from Labarai