On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sanata Ifeanyi Ubah Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hari Da Aka Kai Masa

SANATA IFEANYI UBAH

Rahotanni na baiyana cewa, An halaka jami’an yansanda da kuma Dogarawan Sanata Ifeanyi Uba da har yanzu ba’a tantance yawansu ba, akan hanyar Enugu Ukwu dake cikin karamar hukumar Njikoka a jihar hukumar Anambra.

Wata majiya ta fadawa manema Labarai cewa, Yan ina da kisan sun bude wuta akan ayarin motocin sanatan, inda suka  kashe  jami’an yansanda  da kuma dogarawan  sanatan masu yawan gaske.

Duk da cewar kawo yanzu babu cikakken  labarin yadda abun ya faru a daren jiya, sai wata majiya na baiyana cewa  Makasan sunyi   yunkurin halaka Sanatan ne.

Kakakin rundunar  yansandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai tabbatar da adadin wadanda abun ya ritsa dasu ba kawo yanzu da muke baku labarin.

 

 

More from Labarai