On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Sanata Ike Ekweramadu Da Matarsa Sunyi Karar Hukumar Kula Da Shige Da Fice Da Hukumar Samar Da Shaidar ‘Dan Kasa Dake Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da uwargidansa, Beatrice, sun yi karar hukumar samar da shaidar dan kasa da hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasa da kuma wasu bankunan kasuwanci guda biyu a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

Lauyan su, Adegboyega Awomolo SAN shine ya shigar da karar a gaban Mai shari’a Inyang Ekwo, a bisa zargin da hukumomin Burtaniya ke yi musu na cire sassan jikin David Nwamini.

Sun roki kotu da ta ba da umarni ga hukumar NIMC ta fito da takardar David Ukpo Nwamini domin gudanar da bincike kan laifukan da ake zargi.

Lauyan ya kuma roki kotun da ta bada  umarnin ga wasu bankunan kasuwanci guda biyu da su ba da kwafin takardar da ya yi amfani da ita wajen   bude asusun ajiya.

Sai dai mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 1 ga watan Yuli domin sauraron karar.