On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sanata Natasha Ta Zargi Gwamnan Kogi Da Yunkurin Halaka Ta

Zababbiyar sanatar kogi ta tsakiya da kotun daukaka kara ta tabbatar da nasararta a jiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ta zargi gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da hada makarkashiyar cutar da ita a yayin zaben sanatoci da aka yi cikin watan Maris din bana.

Ta yi wannan zargin ne a  ranar  Talata  ta cikin shirin Siyasa  a yau, na gidan Talabijin na channels, Ta  ce  ta jiwo karar harbin bindiga akan motar  da  take ciki,  kuma  da  bidiyo a matsayin hujjar  da zata  tabbatar da zargin nata.

Ta yi zargin cewar  mutanen da suka rika harbin motar  tata  suna  sanye ne da  riga mai dauke da tambarin jam’iyyar  APC , Kuma daya daga cikinsu  shine baturen zabe na karamar hukumar Okehi.

Haka zalika sanata  Natasha Akpoti ta yi zargin cewar da gangan gwamnan jihar  ya lalata wasu hanyoyi  dake cikin jihar, domin kawo  tazgaro wajen gudanar da zaben.