On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sanata Rufa'i Sani Hanga Ya Maye Gurbin Shekarau A Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya

SANATA RUFA'I SANI HANGA

Sanata Rufa’I Hanga ya samu tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.

Hanga ya samu tikitin ne domin maye  gurbin da Sanata Ibrahim Shekarau ya bari, bayan ficewarsa daga cikin jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

An tabbatar da Sanata Rufa’I Hanga a matsayin Dan takarar ne Sanatan Kano ta tsakiya a cibiyar koyawa matasa sana’oi ta Sani Abacha dake nan Kano, bisa jagorancin shugaban jam’iyyar NNPP na kano ta tsakiya Abdullahi Zubair, wanda daruruwan magoya bayan jam’iyyar daga Kananan Hukumomin 15 suka shaida.

SANATA HANGA

Manyan jagororin jam’iyyar PDP cikinsu hadda tsohon Mataimakin Shugaban kasa, kuma dan Takararta na shugaban Kasa, Atiku Abubakar suka zo nan jihar Kano domin Karbar Sanata Shekarau da ya koma jam’iyyar.

More from Labarai