On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sanatocin APC 22 Na Shirin Ficewa Daga APC

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu Ya baiyana damuwarsa akan yadda ake samun Karin Ficewar Yan Majalisar Dokokin Taraiyya daga cikin Jam’iyyar zuwa Jam’iyyu Hamaiyya.

Shugaban ya baiyana haka a ranar laraba, wata ganawar sirri da  ‘Ya’yan jam’iyyar ta APC da aka yi a Abuja, Babban birnin Taraiyya.

Ya kara da cewa a yayin da jam’iyyar  ke damuwa da ficewar da ake samu daga cikin, to  sai dai kuma babu wani abu da za’a iya yi akan hakan.

Kazalika Yace sauyin sheka da ake samu musamman a lokacin Kakar zabe abune na Al’ada, Kasancewar wadanda suke kallon ba’a yi masu daidai ba a sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyunsu, nada ‘yancin da zasu iya  gwada sa’arsu a sauran jam’iyyu.

Hakan na zuwa ne a yayin da tsohon Ministan Sufurin jiragen Sama na Kasa, Femi Fani Kayode ya tabbatar da cewa akwai karin wasu Sanatocin jam’iyyar 22 dake shirin komawa jam’iyyar  PDP, Inda ya bukaci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dasu dakile wannan yunkuri.

More from Labarai