On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Sanatocin Najeriya Sun Sadaukar Da Albashinsu Na Watan Disamba Ga Mutanen Garin Tudun Biri

Majalisar dattawa ta 10 ta bayar da gudunmuwar naira miliyan 109 ga wadanda harin bama-bamai n kuskure ya rutsa da su a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da bayar da tallafin a lokacin da ya jagoranci wasu manyan hafsoshi da sanatoci a ziyarar jaje ga gwamna Uba Sani kan al’amarin a ranar Lahadi.

Ya ce tallafin da aka bayar domin j wadanda abin ya shafa ya biyo bayan matakin sadaukar da gabaki daya  albashin ‘yan majalisar Dattijai na watan Disamba.

Yayin da yake jajantawa al’ummar yankin Tudun Biri kan wannan mummunan al’amari, Barau Jibrin ya ce majalisar dokokin kasarnan za ta hada kai da fadar shugaban kasa domin bankado al’amuran da suka dabaibaye al’amarin domin kaucewa sake faruwar hakan a nan gaba.