On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Sarkin Bichi Ya Bukaci Gwamnati Ta Kaiwa 'Yan Kasuwa Dauki, Yayin Ziyarar Jaje A Kasuwar Badume Da Ta Fuskanci Tashin Gobara

Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero ya bayyana gobarar da ta tashi a kasuwar Badume da ke karamar hukumar Bichi a matsayin wani mummunan hadari ga tattalin arzikin masarautar.

Sarkin wanda ya kai ziyarar jajantawa kasuwar ya nuna damuwa da irin asarar da akayi sakamakon gobarar.

Sarkin wanda Dandarman Bichi Alhaji Abdulhamid Ado Bayero ya wakilta ya bayyana cewa ya damu matuka da labarin faruwar lamarin.

Yayin da yake kira ga  karamar hukumar da gwamnatin jihar Kano da su bayar da agajin gaggawa ga wadanda gobarar ta shafa, Sarkin ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kawo dauki ga wadanda abin ya shafa, ya kuma kare masarautar daga faruwar irin al'amarin nan gaba.

More from Labarai