On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sarkin Kano Alhaji Dr Ado Bayero Ya Cika Shekara 9 Da Rasuwa

A rana irin ta yau 6 ga watan Yuni na shekarar 2014 Allah  ya yiwa sarkin na 13 a daular Fulani rasuwa yana  da shekara 84.

An haifeshi ranar 25 ga watan Yuli shekara ta 1930 ya rasu 6 ga watan Yuni a shekara ta 2014.

Sarkin Kano ne tun daga shekara ta 1963 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 2014.

Bayero ya kasance kafin ya zama sarkin kano shahararren ɗan kasuwa, kuma yayi aikin banki, sannan  tsohon ɗan sanda ne kuma yayi aiki a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Senigal.