On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

SERAP Ta Gargadi INEC Kan Laifukan Da Suka Shafi Zabe

Kungiyar SERAP mai rajin tabbatar da Adalci da yaki da rashawa a hukumomi da ma’aikatun gwamnati,  ta bukaci Shugaban hukumar zabe takasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya nada lauya mai zaman kansa da zai binciki zargin tashe-tashen hankula a zabe da sauran laifukan zabe a lokacin babban zaben da aka kammala na 2023.

SERAP ta kuma bukaci Yakubu da ya zakulo wadanda ake zargi da aikata laifin da masu daukar nauyinsu, tare da tabbatar da gurfanar da su a gaban kotu, ba tare da la’akari da matsayinsu na siyasa ko alakarsu ba.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 25 ga Maris, 2023, mai dauke da sahannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce wadanda ake zargi da aikata laifin da masu daukar nauyinsu sun aikata laifin da ya saba wa tanadin tsarin mulki da kuma dokar zabe.

Kungiyar ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan al’amarin idan hukumar ta gaza yin aiki da shawarwarin.