On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaba Buhari Ya Bada Umarnin Fara Shirin Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnati A Najeriya Bayan Zaben 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sakataren gwamnatin tarayya da ya ci gaba da bita da tantance ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamnati a zango na uku da hudu na shekara ta 2022 dake kasancewa duk bayan watanni uku.

Ya ce rahotannin ayyukan za su kasance wani bangare na takardun mika mulki ga gwamnatinsa mai barin  gado.

Shugaban ya ba da umarnin ne a ranar Talata a wurin rufe taron sake bibiyar ayyukan ministoci na shekarar 2022.

Ya umurci dukkan ministoci da manyan sakatarori su tabbatar da cewa an mika rahoton ayyukan ma’aikatunsu a duk wata-wata ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya domin  dubawa na nazari akai.