On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaba Buhari Yace Gwamnatinsa Na Kokarin Magance Tsadar Kayan Abinci

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban kasa muhammadu Buhari yace gwamnatinsa, na kokarin magance tashin farashin kayyakin abinci a fadin kasa.

Shugaban  kasa Buhari  ya  baiyana   haka  ne  Ya yin  Bude  bitar kara   sanin  makamar aiki da aka shiryawa   ma’aikatu  karo  na  Ukku domin   sanin  irin   cigaban  da  aka  samu   yayin  aiwatar   ta bangaren aiwatar da manufofinsa    Gwamnatin sa  Guda 9.

Farashin  abinci  ya tashi  zuwa  kaso 23.34  Bisa  Dari,  abisa  kiyasin   shekara zuwa  shekara  wanda  ya kama  kaso   3.77  Bisa  Dari inda  ya  zarta  abunda  aka  samu  a  shekarar  data  gabata  a  cikin   watan  satumba  wanda  ya  kama kaso 19.5  bisa  Dari.

Yayin  Taron ,  shugaba  Buhari  yace  an  Gudanar  da  manyan  ayyuka  a  fadin  kasa,  Wadanda  zasu  cika  burukan  da  ‘yan  Najeriya  suka  sanya  a gaba.