On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Masu Cutar Daji Ta Biliyoyin Naira A Jihar Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da cibiyar kula da cutar daji da akafi sani da Cancer a Jihar Kano mai dauke da kayana aiki biliyoyin naira kafin karshen watan gobe na Oktoba.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa shine ya bayyana hakan a karshen mako yayin da yake zantawa da manema labarai gabanin bikin makon kiwon lafiya na jihar Kano  da aka shirya farawa a yau.

Ya bayyana cewa  an kusa kammala ginin cibiyar da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke aiwatarwa.

Da yake mayar da martani game da kalubalen da ke tattare da aiwatar da shirin asusun kula  da lafiya kyauta ga marasa karfi na gwamnatin tarayya a Kano, Kwamishinan yace hukumomin biyu, da suka hadar da hukumar kula da lafiya matakin farko ta da hukumar taimakakekeniyar lafiya ta jihar KCHMA da ke kula da aiwatar da shirin  suna aiki tukuru don gyara matsalolin.

More from Labarai