On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugaba Tinubu Ya Bada Tabbaci Ga Masu Zuba Jari A Najeriya Daga Kasashen G20

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jan hankalin masu zuba jari daga kasashen G20 cewa Najeriya a shirye take ta hada kai da su, yana mai ba su tabbacin cewa kudadensu na cikin aminci a  harkar kasuwancin kasarnan.

Shugaban kasar ya bayyana a ranar Litinin cewa, bayan albarkatun kasa, Najeriya tana da masu ilimi da  ƙwararru da ƙwazo, waɗanda su ne babban abin da ƙasarnan ke amfani da su wajen fintinkau ga  sauran ƙasashe.

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa a Berlin, Tinubu ya ce yawan al’ummar Najeriya ne suka fi karfafa masu zuba jari kamar yadda aka nakalto a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya sanya wa hannu.

Tinubu ya ci gaba da cewa, Afirka ta zarce batun jita-jitar  cewa rashin bin doka da oda na hana masu zuba jari da karya musu gwiwa.