On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Shirin Karin Kudin Lantarki A Najeriya - Minista

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aiwatar da karin kudin wutar lantarki tare da dagewa cewa za a bada tallafin wutar lantarki a fadin kasarnan.


Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a wani taron manema labarai a Abuja.
Adelabu ya yarda cewa rashin aiwatar da jadawalin farashin yana haifar da matsalar rashin ruwa a fannin, amma ya jaddada cewa shugaban kasar ya ki bada damar karin kudin wutar lantarki.
A wani bangaren, ministan ya sha alwashin yin bincike kan halaccin tsawaita lasisin na tsawon shekaru biyar da aka baiwa kamfanonin rarraba wutar lantarki da samar da wutar lantarki, yana mai jaddada cewa lasisin gudanar da aikinsu ya kare ne a ranar 31 ga Oktoba na  2023.

Haka na zuwa a lokacin da, gwamnatin Tarayya ke shirin samar da ƙarin megawatts 700 a kasarnan domin haɓakawa da faɗaɗa makamashi.

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai.

Adelabu ya ce karin megawatt din zai fito ne daga tashar wutar lantarki ta Zungeru.