On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaba XI Jinping Na China Da Vladimir Putin Na Rasha Zasu Tattauna Kan Yakin Kasar Ukrain

shugaba xi na Sin da Vladimir na Rasha

shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su tattauna kan yakin Ukraine da sauran batutuwan kasa da kasa a taronsu na ranar Alhamis.

Kasashen biyu za su gana ne a kasar Uzbekistan a wani taron koli da zai mada hankali  kan dangantarsu da kasashen yammacin duniya. Mista Xi yana yin ziyararsa ta farko zuwa ketare tun  bayan  barkewar cutar korona.

A yau Laraba ne Xi ya fara ziyarar kwanaki uku a kasar Kazakhstan.

Daga nan zai gana da Mista Putin a ranar Alhamis a taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a Samarkand, wanda zai gudana daga 15 zuwa 16 ga  watan  Satumbar da muke ciki.