On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban INEC A Jihar Adamawa Zai Gurfana A Gaban Kwamiti Na Musamman Bayan Azarbabin Ayyana Binani

Yanzu haka dai kwamishinan zabe na hukumar INEC reshen jihar Adamawa Hudu Yunusa-Ari na cikin tsaka mai wuya bayan  ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar ba bisa ka'ida ba.

A ranar Lahadi ne da karfe 1 na dare  INEC ta mayar da sanarwar sakamakon zaben jihar da aka kammala  zuwa karfe 11 na safe bayan da aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 11 cikin 20 da aka sake gudanar da zaben.

Amma kafin karfe 11 na safe kwamishinan  da karfe 9 na safe ya zo ofishin INEC dake birnin Yola, inda ake tattara sakamakon zaben inda ya ayyana  ‘yar takarar jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna na Jihar Adamawa.

Kafin ayyana ta, Binani tana bin bayan  Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP, wanda ya bata tazarar kuri’u dubu 31 da 249.

Sai dai INEC a cikin sanarwar gaggawa da ta fitar, ta soke matakin Ari tare da kira ga  'yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar a cibiyar tattara sakamakon zaben.

Haka kuma INEC tayi sammcin kwamishinan hukumar na Adamawa da jami’an tatttara sakamakon zaben harma da  wasu jami’ai zuwa birnin Abuja.

Bayanai sunce kwamishinan na INEC zai  gurfana a gaban kwamitin hukumar karkashin jagorancin shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu a yau.