On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaban INEC Zai Gabatar Da Jawabi A Cibiyar Chatham Ta Ingila - Zaben 2023

A yau Talata shugaban hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Mahmood Yakubu zai yi jawabi a cibiyar Chatham da karfe biyu na rana agogon Najeriya.

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi alkawarin wargaza rashin tafiyar da harkokin gudanarwa yadda suka kamata tare da kawar da manufofi da ke haifar da cin hanci da rashawa.

Shahararriyar cibiyar manufofin kasa da kasa ta Burtaniya, tace taron wani bangare ne na ayyukan duba akan  zabukan Najeriya da ci gaban siyasa a shekarar 2023.

Shugaban na INEC zai yi magana ne game da shirye-shirye da abubuwan da suka sa a gaba domin tabbatar da ingancin zabe.

Tunda farko dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi jawabi a cibiyar ranar Litinin, inda ya ce gwamnatinsa za ta wargaza tasirin aikata laifuka da akayi amfani da su wajen durkusar da kasarnan.

Dangane da yadda yake da niyyar tunkarar yiwuwar samun Majalisar Dokoki ta kasa wacce wasu jam’iyyu zasu mamaye, Obi yace ya samu irin wannan gogewa a matsayin gwamna lokacin da babu daya daga cikin ‘yan majalisar jihar 30 da ya fito daga jam’iyyarsa.

Yace matakan da za’a bi wajen  magance irin wannan al’amari shi ne a yi abin da ya dace, a kaucewa son zuciya domin su ma ‘yan majalisa suna son shugabanci na gari.

More from Labarai